‘Yan bindiga sun sace matan shugaban ƙaramar hukuma

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa tare sace matansa guda biyu.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Nasiru Ahmed Kiyawa – wanda ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin – ya ce ‘yan bindigar sun je gidan nasa ne bayan sallar Isha’i a ranar Juma’a daddare, inda suka kore mutanen da ke kofar gidan nasa kafin su shiga ciki.

Ya ƙara da cewa “sau biyu suna harba bindiga a ƙofar gidana kafin su shigo ciki”.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga bakwai a Kaduna

Daga nan ne kuma suka tafi da matan nasa guda biyu, inda kuma har yanzu suke garkuwa da su, kamar yadda ya tabbatar wa BBC.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Adam Shiisu ya tabbatar wa BBC faruwar lamarain, inda ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta samu ƙiran gaggawa kan lamarin, inda kuma nan take suka tura jami’ansu domin kai ɗauki.

Sai dai kafin zuwan jami’an na ‘yan sanda tuni ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matan shugaban ƙaramar hukumar.

DSP Shiisu ya ce tuni rundunar ‘yan sanda jihar ta baza jami’an a lungu da saƙo na ƙaramar hukumar domin kuɓutar da matan.

Ya kuma ce rundunar ‘yan sandan na maraba da duk wasu bayanai da za su taimaka wajen kai ga gano masu garkuwan don kuɓutar da matan.

Matsalar garkuwa da mutane dai wani baƙon al’amari ne a jihar ta Jigawa, to sai dai matsalar na neman kunno kai cikin jihar a baya-bayan nan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *