‘Yan bindiga sun sace manoma 11 a Abuja

0
185

’Yan bindiga sun sace manoma 11 a yankunan Achimbi da Gumanyi da ke Kwaku a yankin Kuje a Abuja.

Wani mazaunin Achimbi, Yunusa Aliyu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da misalin karfe 11:00 na safe lokacin da manoman suke girbin doya a gonakinsu.

Ya ce ’yan bindigar ɗauke da muggan makamai ba zato ba tsammani suka kewaye su, nan take suka yi awon gaba da su.

Aliyu, ya ce ’yan bindigar sun fara sace wani manomi a wata gona da ke Gumanyi kafin su wuce Achimbi su yi awon gaba da wasu 10 a can.

Ya ce ya zuwa yanzu maharan ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka sace ba, domin neman kuɗin fansa.

KU KUMA KARANTA: Yankunan Bwari, Kuje da Abaji suka fi haɗarin rayuwa a Abuja – FCTA

Ya ƙara da cewa shugaban maharan ya ce ba zai yi magana game da kuɗin fansa ba har sai ya gana da shugaban ƙauyen Achimbi.

“Kuma yanzu mun ruɗe saboda shugabansu ya ce ba zai yi magana game da kuɗin fansa ba har sai ya gana da shugaban ƙauyenmu.

“Kuma shugaban ƙauyen nan ya yi tafiya ba ya nan, duk da cewa ana sa ran zai dawo yau Lahadi ko Litinin,” in ji shi.

Lokacin da aka tuntuɓi, kakakin rundunar ’yan sandan birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ta ce ba ta da masaniyar faruwar lamarin.

Amma ta yi alƙawarin yin ƙarin haske da zarar ta samu bayani.

Leave a Reply