‘Yan bindiga sun kashe ‘yan Banga 12, sun sace mutane da dama

0
13
‘Yan bindiga sun kashe ‘yan Banga 12, sun sace mutane da dama

‘Yan bindiga sun kashe ‘yan Banga 12, sun sace mutane da dama

Daga Idris Umar, Zariya

Wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a unguwar Sabuwar Tunga da ke unguwar Adabka a ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara a ranar Talata, inda suka yi garkuwa da mutane huɗu.

Majiyoyi sun bayyana cewa, ‘yan banga na yankin sun yi gaggawar daukar matakin dakile harin tunda farko. Sai dai a yayin da suka bi maharan zuwa cikin daji, ‘yan bindigar sun yi harin kwantan bauna inda suka kashe ‘yan banga 12.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mata da ƙananan yara a Zamfara

Wata majiyar a yankin ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi galaba a kan ‘yan banga a lokacin da suka yi musu kwanton bauna, inda suka yi musu barna sosai kafin su koma cikin dajin.

“Da farko dai al’ummar garin sun fatattake su, amma abin takaici sai ‘yan bindigar suka sake haduwa suka yi wa mutanen mu kwanton bauna, lamarin da ya yi sanadin rasa mambobinmu 12,” inji majiyar.

Leave a Reply