‘Yan bindiga sun kashe wasu mutane a Nijar

Mutum goma sha ɗaya ne suka mutu a hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙauyuka biyu na Jamhuriyar Nijar da ke kan iyaka da Burkina Faso a ƙarshen mako, a cewar sanarwar da ma’aikatar tsaron ƙasar ta fitar ranar Lahadi.

“’Yan ta’adda a kan babura da dama sun kai hari a ƙauyukan Amara da Loudji,” masu nisan kilomita 30 a kudu maso gabashin Bankilare, “inda suka kashe mutum 11,” in ji sanarwar.

Sun kai harin ne a yayin da jami’an tsaron Nijar suka “ƙaddamar da jerin hare-hare” ranar Juma’a, waɗanda ma’aikatar tsaron ta ce “sun lalata ɗaukacin” hanyoyin sadarwar ‘yan ta’addan.

Ta ƙara da cewa an kashe soja ɗaya tare da jikkata guda biyar ranar Juma’a lokacin da motarsu da ke yin sintiri ta taka nakiya a kauyen Ouro Gueladjo, mai nisan kilomita 70 daga Yamai, babban birnin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 4 suka sace 39

Tun daga watan Yuli sojoji suke mulki a Nijar bayan sun kifar da gwamnatin farar-hula.

Ranar 17 ga watan Disamba, shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya ce ƙasar tana “samun ci-gaba” wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa sojoji sun samu “nasarori da dama” ta hanyar daƙile tarzoma.

Sojoji da mazauna yankunan da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali sun ce an samu kwanciyar hankula a makonnin da suka gabata.

A watan Oktoba an kashe sojoji shida a kan iyakar Nijar da Burkina Faso sakamakon ba-ta-kashi da ‘yan bindiga.

Kazalika a watan na Oktoba, an kashe sojojin Nijar 29 a hari mafi muni da ‘yan bindiga suka kai musu tun bayan juyin mulkin da soji suka yi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *