No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe Malam Usman Sarki, hakimin garin Zazzaga da ke ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.

Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya cewa ‘yan bindigar sun ƙaddamar da harin ne a Zazzaga da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su a daren Talata, 10 ga Oktoba, 2023.

Majiyar ta ce an kuma yi garkuwa da wasu manoma da ba a tantance adadinsu ba ciki har da mata.

“An kai harin ne cikin dare ranar Talata.  Sun harbe Hakimin ƙauyen na Zazzaga, Malam Usman Sarki har lahira tare da yin garkuwa da wasu da dama,” inji majiyar.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

“A yanzu, ba za mu iya bayar da ainihin adadin mutanen da suka tafi da su ba.  Sun kuma yi awon gaba da shanu da awaki da tumaki da yawa namu.”

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan harin da ake zargin an kai ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...