‘Yan bindiga sun kashe wani da su ka yi garkuwa da shi, saboda rashin isasshen kuɗi a asusunsa na Banki

0
229
'Yan bindiga sun kashe wani da su ka yi garkuwa da shi, saboda rashin isasshen kuɗi a asusunsa na Banki

‘Yan bindiga sun kashe wani da su ka yi garkuwa da shi, saboda rashin isasshen kuɗi a asusunsa na Banki

Jami’an rundunar yansandan jihar Delta sun kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da wani mutum bayan sun karɓi kudin fansa na Naira miliyan biyu (₦2,000,000) daga hannun sa, amma duk da haka su ka harbe shi.

Wadanda ake zargin, wato Chukwuebuka Nka, mai shekaru 25, Uche Okechukwu, da Somto Chukwuma, sun harbi wanda suka sace din a ƙafarsa bayan sun gano cewa ba shi da isasshen kuɗi a cikin asusun sa na banki.

A cewar mai magana da yawun rundunar ƴansandan, Bright Edafe, kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan samun rahoton gaggawa cewa wani matashi an sace shi daga gidansa a Ogwashi-Uku.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Katsina sun kashe masallata 13

Ya bayyana cewa jami’an sun bi sahun masu garkuwa da mutane har zuwa daji a Ogwashi-Uku, inda aka ceto wanda aka sace tare da raunin harbin bindiga.

Edafe ya ce bincike ya kai ga kama Chukwuebuka Nka da Uche Okechukwu a jihar Anambra, inda aka kuma gano motar wanda aka sace din kirar Toyota Venza.

Ya ƙara da cewa bisa ga amsar da waɗanda ake zargin suka bayar, jami’an ƴansanda sun kai samame matsuguninsu da ke kauyen Agidiase, Ogwashi-Uku, inda aka kama na ukun.

Masu laifin sun jagoranci ‘yan sanda zuwa maboyarsu, inda aka gano motar da suke amfani da ita wajen aikata laifuka da kuma wata na’urar da ke tare sabis din sadarwa.

Leave a Reply