No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

A jamhuriyar Nijar sojojin ƙasar sama da 10 ne suka rasa rayukansu yayin wasu hare-hare biyu da ‘yan bidiga suka kai a yankin Tillabery.

Sai dai in ji rahotanin da suka fito daga yankin na kan iyakokin ƙasashen uku sojojin Nijar sun kashe ‘yan bindigar da dama yayin wani luguden wuta da suka musu ta jiragen yaƙi.

Rahotanin daga yankin na Tillabery na cewa da misalin ƙarfe 9 na safiyar yau Alhamis ne wasu mutane da ake kyautata zaton cewa ‘yan ƙungiyoyi masu iƙirarin jahadi ne da suka yi kaka-gida a wannan yanki na kan iyakokin ƙasashen uku suka auka wa wani sansanin sojojin ƙasar dake Kandadji a Jahar ta Tillabery.

Sojojin ƙasar 12 ne suka mutu yayin wannan ɓarin wuta irin na mai kan uwa da wabi, an kuma jikkata sojojin bakwai, yayin da aka nemi biyu aka rasa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...