‘Yan bindiga sun kashe masu haƙa ma’adinai a jihar Filato

An harbe wasu ma’aikatan haƙar ma’adinai uku a ranar Juma’a a wani wuri da ke kusa da Tanjol a unguwar Jol da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato a ranar Juma’a.

Rwang Tengwong, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Matasan Berom (BYM), ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Asabar, inda ya ƙara da cewa sauran masu haƙar ma’adinai da manoma da ke kusa da su sun gudu daga yankin.

A cewar Tengwong, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe, ya ƙara da cewa wasu mutane biyu sun samu raunuka.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata mata da yaran da suka dawo daga ƙasar waje a Kwara

Sakataren yaɗa labaran wanda ya bayyana harin a matsayin wanda ya yi yawa, ya yi ƙira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar karkara.

Ya ce duk da tura jami’an ‘yan sandan tafi da gidanka a yankin, ana ci gaba da kashe-kashe ba tare da tsayawa ba.

DSP Alfred Alabo, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Filato, bai samu ƙiran layinsa da dama ba, amma wani babban jami’in ‘yan sanda ya tabbatar da faruwar harin.

An kashe fiye da mutane 200 kwanan nan a ƙauyukan Mangu, Barikin Ladi da Riyom na jihar.


Comments

2 responses to “‘Yan bindiga sun kashe masu haƙa ma’adinai a jihar Filato”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe masu haƙa ma’adinai a jihar Filato […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe masu haƙa ma’adinai a jihar Filato […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *