Shugaban ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, Joseph Hayab, ya ce ‘yan bindiga sun kashe fastoci 23 tare da rufe coci sama da 200 a faɗin jihar Kaduna.
Mista Hayab ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Musa Garba, da limaman coci-coci daban-daban na ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Shugaban na CAN ya bayyana cewa cocin ya shiga mawuyacin hali sakamakon ayyukan masu aikata laifuka a jihar.
Ya ce: “Wani Fasto da aka yi garkuwa da shi a ranar 8 ga Agusta 2023, ya shaida wa shugabannin CAN cewa akwai Kiristoci sama da 215 da ‘yan bindigar suka sace a dajin Birnin Gwari.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Kebbi sun kashe mutane biyu, sun sace mutane bakwai
“Har yanzu suna nan kuma Fasto ya shaida mana cewa ‘yan bindigar sun nemi ya yi addu’a ga Kiristoci 215 a lokacin da yake cikin kogon su.
“Muna ƙira ga Kwamishinan ‘yan sanda, da ya duba wannan batu a tsakanin sauran mutane gaba ɗaya don ƙara ƙarfafa ƙwarin gwiwar jama’a,” in ji Mista Hayab.
Shima da yake jawabi, tsohon babban sakataren ƙungiyar Evangelical Church Winning All, (ECWA), a faɗin duniya, Yunusa Nmadu, da sauran limaman cocin da suka yi jawabi a wurin taron sun buƙaci kwamishinan ‘yan sandan ya kuma yi la’akari da kamo limamai da suka tsunduma cikin wa’azin ƙiyayya da kalaman ƙiyayya.
Limaman sun yi ƙira ga kwamishinan ‘yan sanda da ya duba lamarin masu sayar da miyagun ƙwayoyi, inda suka ce galibin laifukan ana aikata su ne ta hanyar amfani da miyagun ƙwayoyi.
Da yake mayar da martani, kwamishinan ‘yan sandan, ya jaddada cewa aikata laifuka ba shi da addini, yana mai cewa duk wanda ya aikata wani laifi to a ƙira shi a matsayin mai laifi ba tare da bayyana shi a matsayin Kirista ko Musulmi ba.
“Tsaro alhakin kowa ne ba na gwamnati kaɗai ba. Yayin da gwamnati ke kan gaba wajen kare rayuka da dukiyoyi, ana kuma sa ran ɗaiɗaikun mutane za su taka rawar gani musamman a fannin samar da bayanai.
“Taron ya kasance don ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ‘yan sanda da shugabannin addini da sauraron ƙalubalen da suke fuskanta tare da samar da hanyoyin da za a iya magance su.
“Rundunar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancina a jihar za ta yi iya ƙoƙarinta wajen gudanar da ayyukanmu. Ya kamata mu zama masu kiyaye ’yan’uwanmu.
“Koyaushe ku tuntuɓi jami’an tsaro da ke kewaye da al’ummomin ku da bayanan gaggawa da zarar kun gano mutanen da ake tuhuma,” kwamishinan ya umarci limaman.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe fastoci 23, sun rufe coci sama da 200 a Kaduna – Ƙungiyar CAN […]