‘Yan bindiga sun kashe Fasto da mutane 20 a Filato

Wasu ‘yan mutane ɗauke da bindigogi, waɗanda ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe Rabaran Nichodemus Kim na Cocin Christ in Nation (COCIN) da wasu mutane 20 a ƙananan hukumomin Riyom da Barikin Ladi da ke jihar Filato.

An kashe faston ne a unguwar Gana-Ropp da ke Barikin Ladi, yayin da kuma aka yi ɓarna a ƙauyukan Rim, Jol, da Kwi na Riyom.

Rwang Tengwong, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar Berom Youth Movement, (BYM), wata ƙungiyar al’adu da zamantakewa, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Talata a Jos.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun sace Hakimai biyu a Bauchi

A cewar Mista Tengwong, an kai wa al’ummomin hari a lokaci guda, inda ya ƙara da cewa hare-haren sun kasance a tare.

Ya yi bayanin cewa hare-haren da suka auku a daren Lahadi, sun yi sanadiyyar jikkata mutane da dama, inda ya ce a halin yanzu an raba mutane da dama da matsugunansu.

“Mutane 21 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a ranar Lahadin da ta gabata yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ƙauyukan Rim, Jol, Kwi na Riyom da kuma Gana-Ropp a Barikin Ladi. “An kashe mutane biyu a Rim, Bakwai a Jol, 11 a Kwi, duk a Riyom, yayin da wani limamin coci, Rabaran Nichodemus Kim, aka kashe a Gana-Ropp Barikin Ladi.

“Hare-haren da aka kai a Rim, Jol da Kwi an haɗa su ne a lokaci guda kuma an gudanar da su a tsakanin ƙarfe 2 na rana da ƙarfe 7 na yamma.
“A Kwi, an lalata dukkanin al’umma, Hei-gwe, kuma an lalata gonaki fiye da 100,” in ji shi.

Tengwong ya yi ƙira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su samar da mafita mai ɗorewa ga yawaitar hare-hare da kashe-kashe a cikin al’ummomi.

“ƙungiyar BYM ƙarƙashin jagorancin Solomon Mwantiri, ta haka ne ta yi Allah-wadai da hare-haren haɗin gwiwa da sauran nau’ukan tada zaune tsaye da ake kaiwa mutanen Filato tun bayan zaɓen 2023.

“Muna ƙira ga sabuwar gwamnati a matakin tarayya da jihohi, da su ɓullo da sabbin dabarun magance matsalar tsaro a ƙasar nan musamman a Filato.

“Har ila yau, dole ne jami’an tsaro su farka kan nauyin da ya rataya a wuyansu na kare rayuka da dukiyoyi. “BYM ta kuma yi ƙira ga al’ummar Berom da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda, amma dole ne su binciki duk wata hanya da za ta kare al’ummarsu saboda ba za mu iya zama muna kallo yayin da suke kashe mu ɗaya bayan ɗaya ba,” inji shi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya kasa samun jin ta bakinsa. Sai dai, Caleb Mutfwang, gwamnan jihar, ya tabbatar da kashe-kashen a cikin wata sanarwa da Gyang Bere, Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, DOPPA, ya fitar.

Gwamnan ya kuma tabbatar da yin garkuwa da wani basarake a Mushere da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar.

Ya kuma yi wa al’ummar jihar alƙawarin dagewa wajen magance yawaitar hare-hare da kashe-kashe da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu.
“Bari na tabbatar wa jama’a cewa muna sake gyara jami’an tsaro na jihar kuma da yardar Allah za mu samu zaman lafiya a Filato,” inji shi.

Gwamnan ya yi ƙira ga mazauna jihar da su nisantar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu su haɗa kai domin ciyar da jihar gaba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *