‘Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ‘yan jarida a Yobe, sun harbi ɗan sandan da ke gadi a ƙafa
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar yau, inda suka harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar.
Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na safe, inda maharan suka buɗe wuta, inda suka yi wa jami’in rauni a ƙafa. Yanzu haka yana jinya a sashin gaggawa na asibitin ‘yan sanda dake Damaturu.
Shugaban ƙungiyar NUJ reshen jihar Yobe, Kwamared Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali da kuma babbar barazana ga lafiyar ‘yan jarida a jihar. Ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da maharan a gaban kotu.
KU KUMA KARANTA: Kwamishinan yaɗa labaran Yobe, Bego ya yaba wa Gwamna Buni kan nuna goyon baya ga ‘yan jarida (hotuna)
Ƙungiyar ta NUJ ta kuma yi kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro ga ƙwararrun kafafen yaɗa labarai da cibiyoyin yaɗa labarai a faɗin jihar, inda ta jaddada cewa irin waɗannan hare-hare na iya kawo cikas ga ‘yancin ‘yan jarida da kuma samun damar yin amfani da bayanan jama’a.
Rahotanni sun ce hukumomin ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin. Ƙungiyar ta jaddada cewa kare ‘yan jarida na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban dimokuraɗiyya da riƙon amanar jama’a.