Mahara sun kai farmaki kan jama’a a kasuwar Didango da ke ƙaramar Karim Lamiɗo da ke Jihar Taraba.
Wani mazaunin garin, Yakubu Adamu ya shaida wa manema labarai cewa mahara kusan 200 ɗauke da makamai ne suka far wa kasuwar a ranar Laraba, suka kashe mutum biyu, suka jikkata wasu da dama sannan suka wawushe kayayyaki na miliyoyin Naira.
Ya ce a yayin da kasuwar ke tsaka da ci a ranar Laraba ne maharan, waɗanda ake zargin ’yan sa kan wata ƙabila ce, suka far mata bagatatan, “ba tare da an tsokane su ba suka far wa Didango, wanda yawancin mazaunansa Fulani, Hausawa, Jarawa da kuma ’yan ƙabilar Wurkum ne.
Sai dai ya ce matasan Didango sun yi arangama da maharan suka fatattake su, a yayin da wata majiya ta yi zargin an kawo musu harin ne domin tayar da rikicin ƙabilanci a yankin.
Kakakin ’yan sandan Jihar Taraba, SP USman Abdullahi ya tabbatar da harin, amma ya ce mutum ɗaya ne aka kashe.