Jami’ar Jihar Filato, (PLASU), ta ce jami’an tsaronta sun daƙile wani hari da ‘yan bindiga suka kai harabar jami’ar a daren ranar Talata.
Hukumar makarantar ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan kwanan ɗaliban makarantar da ke Bokkos tsakanin daren Talata zuwa Laraba amma ba a yi garkuwa da su ba.
John Agams, jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Najeriya aukuwar lamarin. Mista Agams ya ce masu laifin sun kai hari makarantar ne domin yin garkuwa da ɗalibai amma jami’an tsaro na jami’ar sun daƙile su.
“Gaskiya ne ‘yan bindiga sun yi yunƙurin sace wasu ɗalibanmu, amma jami’an tsaron mu na yankin sun daƙile yunƙurin. “A cikin haka, ɗalibi ɗaya ya samu rauni, amma babu wani ɗalibi da aka sace.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace mahaifin ɗan majalisa a Zamfara
“A halin yanzu mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Benard Matur yana harabar makarantar kuma yana ƙira ga ɗalibai da su kasance cikin lumana,” inji shi. Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba kan lamarin.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari a jami’ar Filato – Jami’a […]