Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun mamaye ƙauyen Agojeju odo dake ƙaramar Hukumar Omala ta jihar Kogi, inda suka hallaka mutane 19 tare da cinnawa gidaje da dama wuta.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya, yace ‘yan bindigar sun auka wa ƙauyen ne a jiya Alhamis.
A cewar William Aya, baturen ‘yan sanda mai kula da ƙaramar hukumar ya shaida masa cewar an hallaka mutane 19 tare da jikkata wasu da dama a harin.
KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga na cigaba da ɗaukar rayuka a jihar Neja
Ya ƙara da cewar, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kogi, Bethrand Onouha, ya tura ƙarin jami’an ‘yan sanda zuwa yankin da al’amarin ya faru, tare da ba da tabbacin farauto waɗanda suka aikata aika-aikar.
A wani labarin kuma, ƙaramar hukumar ta bayyana cewar, ‘yan bindigar sun aukawa ƙauyen Agojeju Odo, a yayin da ƙauyukan dake maƙwabtaka da shi irinsu; Ajokpachi Odo da Bagaji a ƙaramar hukumar ta Omala suka zama kufayi babu kowa a cikinsu.
Ƙauyukan sun buƙaci Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo da hukumomin tsaro su kawo musu agaji ta hanyar tura ƙarin jami’an ‘yan sanda zuwa yankin, kasancewar ‘yan bindiga na neman fin ƙarfin ƙaramar hukumar.