’Yan bindiga na neman N16m da babura 4 kan mutane 11 a Kaduna

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 11 a ƙauyen Kubuwo da ke ƙaramar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna, inda suka buƙaci naira miliyan 16 da sabbin babura huɗu a matsayin fansa.

Aminiya ta gano cewa Kubuwo kusa da ƙauyen Kudiri, inda mutanen ƙauyen suka tsare duk da cewa an biya kuɗin fansa miliyan 10.

Wani mazaunin garin Kubuwo, Alkali Danjuma, ya ce ranar Asabar da dare ne ’yan bindigar suka mamaye ƙauyen “a kan babura suna harbi a iska, wasu daga cikinsu suka shiga gidaje uku suka kwashe mutum 11 ciki har da yara uku.”

Ya ce shugaban ’yan bindigar ya ƙira waya da yammacin Lahadi suna neman kuɗin fansa da babura huɗu daga ’yan uwan waɗanda abin ya shafa.

Shugaban ƙauyen Kudirida ke kusa da su, Wakili Iliya, ya ce “da misalin karfe 2 na safiyar yau na samu ƙira cewar ’yan bindiga sun mamaye Kubuwo kuma sun yi awon gaba da wasu mutane.”

Ya roƙi gwamnati da ta kawo musu ɗauki wajen ceto waɗanda aka sace a ƙauyensu.

Babu wani martani a hukumance daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna kan lamarin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *