‘Yan Bindiga a Zamfara, sun buƙaci miliyan huɗu ga ‘yar NYSC da suka sace

3
371

Wasu ’yan bindiga sun buƙaci a biya Naira miliyan huɗu a matsayin kuɗin fansa domin sako ɗaya daga cikin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da aka sace a jihar Zamfara kwanakin baya.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mutane 8 da ke kan hanyarsu ta zuwa sansanin masu yi wa ƙasa hidima na NYSC a jihar Zamfara a ranar Juma’ar da ta gabata.

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa masu yiwa ƙasa hidimar da ke shirin tafiya a cikin wata motar bas ta Akwa Ibom (AKTC) daga Uyo, Akwa Ibom zuwa Jihar Sakkwato, ‘yan fashin sun tare motar su.

Emmanuel Etteh, mahaifin Glory Thomas ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kira shi ta hanyar amfani da lambar wayar su.

KU KUMA KARANTA: Hukumar NYSC ta tabbatar da yin garkuwa da ɗalibai takwas a Zamfara

Sun sanar da shi game da sace ‘yarsa kuma sun buƙaci a biya su Naira miliyan 4 domin a sako ta cikin ƙoshin lafiya.

Etteh ya ce: “Sun ƙira ni da layinsu, sannan suka ce in biya naira miliyan huɗu.

Na nemi in yi magana da ‘yata don tabbatar da cewa tana cikin ƙoshin lafiya.

Sai na tambayi yadda suke so mu biya kuɗin da suka ce mu tuntuɓi AKTC.

“Tun daga wannan lokacin ba su yi waya ba kuma ban yi magana da ’yata ba. Ban sani ba ko sun sake su amma ‘yata ba ta ƙira ni ba.”

Har ya zuwa lokacin da ake wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba ta bayar da wani bayani kan lamarin garkuwa da mutane ba.

Sai dai wani jami’in soji da ba a bayyana ba ya bayyana cewa, tawagar masu aikin ceto na binciken dajin domin ƙwato waɗanda abin ya rutsa da su daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.

3 COMMENTS

Leave a Reply