No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 12 da suka haɗa da mace ɗaya da ‘ya’yanta biyu da kuma sirikanta a ƙauyen Kurya da ke ƙaramar hukumar Rabbah ta jihar Sakkwato.

 Wani mazaunin unguwar, Yusuf Kurya, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari ƙauyen ne a daren Lahadi, 24 ga watan Disamba, 2023.

“Lamarin ya faru ne a daren Lahadi da misalin karfe 8:30 na dare lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari ƙauyen mu da yawa, suna harbi lokaci-lokaci,” kamar yadda ya shaida wa jaridar Punch ranar Talata.

“Sun kashe kusan mutane 12 a yayin da aka kona huɗu daga cikinsu da ransu.

“Sun kuma yi awon gaba da wasu mata uku a ƙauyen yayin da kuma aka yi awon gaba da dabbobi da ba a tantance adadinsu ba.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace manoma 11 a Abuja

Ya ce biyo bayan ƙiran da mazauna yankin suka yi, an tattara dakarun Operation Hadarin Daji inda suka bi su, inda suka kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufa’i, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya ce daga bayanan karshe da ya samu daga ƙauyen, tuni aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai tare da yuwuwar alkaluman su ƙaru.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...