Connect with us

'Yan bindiga

‘Yan bindiga a Kebbi sun kashe mutane biyu, sun sace mutane bakwai

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da suka kai farmaƙi ƙauyen Kwarikwarasa da ke ƙaramar hukumar Maiyama a jihar Kebbi a ƙarshen makon da ya gabata, sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu mutanen ƙauyen su bakwai.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigan sun mamaye al’ummar ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 9 ga watan Satumba.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

Gwamna Nasiru Idris ya ziyarci al’umma inda ya tabbatar da cewa gwamnati ta tanadi matakan daƙile sake aukuwar lamarin.  Ya ce ya bai wa jami’an tsaro dukkan goyon baya da haɗin kan da ya kamata domin yaƙar miyagun ayyuka a faɗin jihar.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: ‘Yan bindiga sun kashe fastoci 23, sun rufe coci sama da 200 a Kaduna – Ƙungiyar CAN | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

'Yan bindiga

Muna ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban jami’ar da ‘yan bindiga suka sace – Gwamnatin Kogi

Published

on

‘Yan bindigar dai sun aukawa jami’ar kimiyya da fasaha ne dake garin Osara a ƙaramar hukumar Adabi a jihar Kogi inda bayan jikkata wasu ɗaliban, sannan suka yi garkuwa da wasu kimanin 57.

Malam Ɗan Asabe wani mazaunin jihar Kogi yace ‘yan bindigar sun haura cikin jami’ar ne ta baya suka dinga harbin kan mai uwa da wabi kamar yadda ya yiwa wakilin Muryar Amurka bayani ta wayar salula.

Tuni dai Gwamnatin jihar Kogin ta yi Allah wadai da wannan hari tare da nuna takaicinta akan lamarin.

Kwamishinan Labarai na jihar Kogin, Kensly Fanwo, yace, kawo yanzu ba su tantance adadin ɗaliban da ‘yan bindigar suka sace ba, amma sun haɗa hannu da jami’an tsaro domin ganin an kuɓuta da ɗaliban cikin ƙoshin lafiya.

KU KUMA KARANTA:’Yan bindiga sun sace ɗalibai a Jami’ar Jihar Kogi

Ya ƙara da cewa, a lokacin da gwamnatin jihar ta samu labarin ta yi ƙoƙarin jibga jami’an tsaro a wannan yanki domin samun nasarar kuɓutar da ɗaliban da aka sace.

A wata sanarwa daga kakakin ‘yan sandan jihar Kogin, Wilyans Aya, ya ce kwamishinan ‘yan sandan ya ƙara tura jami’an tsaro na musamman domin samun nasarar kuɓutar da ɗaliban.

Garkuwa da ɗaliban makaranta dai na ci gaba da ɗaukar hankali a Nijeriya, al’amarin da masana suka ce babbar barazana ce a ɓangaren Ilimi a ƙasar.

Continue Reading

'Yan bindiga

An sace limaman coci 6 a Anambara

Published

on

Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu limaman Coci shida yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Awka na jihar Anambara a kudu maso gabashin Najeriya.

Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun sace Archbishop Uka Uka na Mujami’ar Brotherhood of the Cross and Star, (BCS) da matarsa Anne Osim da ɗansu Ronald Uka Osim.

Sauran limaman Cocin sun haɗa da Azuka Ochu, Moses Okafor da Anderson Akwazie a cewar jaridar Daily Trust.

Jaridar Daily Post ta yanar gizo ta ruwaito cewa mutanen na hanyarsu ta zuwa Awka ne daga jihar Abiya don gudanar da ayyukan wa’azi a lokacin da lamarin ya faru.

Al’amarin ya faru ne a ranar 1 ga watan nan na Mayu kamar yadda rahotanni suka nuna.

KU KUMA KARANTA:An halaka direba da sace mutum 2 a hanyar Abuja

“Mun damu matuƙa, amma muna da tabbacin cewa Ubangijin da suke bautawa zai taimaka musu.” Jaridar ta Daily Post ta ruwaito wani Limami a Cocin ta BCS, Bishop Denis Onuoha yana cewa.

Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar Anambara, ta ce ba ta da masaniyar aukuwar wannan al’amari.

“Ba mu da wasu bayanai da suka nuna aukuwar wannan al’amari a jihar Anambara.” Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce a ranar Asabar ɗauke da sa hannun Kakakinta SP Tochukwu Ikenga.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “muna ƙira ga jama’a da su taimaka mana da bayanai kan wannan al’amari idan har ya faru, hakan zai ba mu dama mu ƙaddamar da bincike.”

Continue Reading

'Yan bindiga

‘Yan bindiga sun kashe mutane 25 a wasu ƙauyuka a arewa maso yammacin Najeriya

Published

on

Wasu ‘yan bindiga daga ƙungiyoyin miyagu sun kashe mutane 25 a lokacin da suka kai farmaki a wasu ƙauyuka huɗu a yankin arewa maso yammacin Najeriya, a matsayin ramuwar gayya saboda farmakin da sojoji suka kai maɓoyarsu, a cewar wani jami’in tsaro a yankin.

A Katsina aka kai hare-haren a ranar Alhamis, jihar da ke daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

‘Yan bindiga sun auka ƙauyukan Unguwar Sarki, Gangara, Tafi da Kore a ƙaramar hukumar Sabuwa da yammacin ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mazauna ƙauyukan, a cewar Nasiru Babangida, kwamishinan tsaro na jihar Katsina.

KU KUMA KARANTA:Harin ‘yan bindiga ya sabbaba kisan mutane 10 da yin garkuwa da masu unguwanni 2 a Kaduna

Mazauna yankin da dama sun jikkata yayin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, a cewar Babangida.

Yawancin garuruwa a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun kafa rundunonin mayaƙan sa-kai ko ‘yan banga domin yaƙar ‘yan bindiga a yankunan karkara da babu jami’an tsaro sosai, kuma ɓangarorin biyu na fafatawa sosai.

A baya-baya nan ‘yan bindigar sun kai farmaki a ƙauyukan ne a matsayin ramuwar gayya saboda hare-hare ta sama da sojojin Najeriya suka kai sansanoninsu a yankin da kuma a maƙwabciyar jihar Kaduna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da ‘yan bindigar 200, inji Babangida.

Ƙungiyoyin da suka ɓoye a dazuzzukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja, sun yi ƙaurin suna wajen sace ɗalibai da yawa a makarantu a shekarun baya-baya nan.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like