Wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu ma’aurata da suka yi aure waɗanda kuma malaman makarantar sakandare ta BECO Comprehensive High School da ke Kwi a ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun kuma raunata mataimakin shugaban makarantar a lokacin da lamarin ya faru a ranar Litinin.
Mista Alabo, wanda bai yi ƙarin bayani kan lamarin ba, ya ce rundunar na kan gaba a lamarin.
A halin da ake ciki, Rwang Tengwong, sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar Berom Youth Movement, a wata sanarwa a ranar Talata, ya bayyana baƙin cikinsa kan lamarin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Zamfara, sun kashe mutum ɗaya, sun sace ɗan sarki da wasu mutane shida
Mista Tengwong ya ce: “Mun yi baƙin ciki da mamayar BECO Comprehensive High School Kwi da ‘yan bindiga suka yi.
“An harbe malamai biyu, Mista da Mrs. Rwang Ɗanladi, sabbin ma’auratan da suka yi aure. “Malam Dalyop Emmanuel, mataimakin shugaban makarantar ya samu munanan raunuka sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai.
“Malaman sun gudanar da taro ne domin tattara sakamakon ɗaliban a shirye-shiryen ranar jawabi da bayar da kyaututtuka na makarantar na shekarar 2023 da aka tsara a wannan Juma’a.
“Wanda ya ji rauni a halin yanzu yana karɓar magani a asibitin koyarwa na jami’ar Jos,” inji shi.
Kakakin ya yi tir da ƙwararan masu aikata laifuka a wasu al’ummomin jihar. “Muna ƙira ga jami’an tsaro da su hanzarta kai farmaƙi ga waɗannan al’ummomi da suka zama gungun ‘yan ta’adda, musamman Fass da Mahanga a Riyom.
“Wannan ya zama dole don kawar da masu aikata laifuka da suka saɓa wa doka da oda,” in ji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a jihar Filato sun kashe sabbin ma’aurata […]
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a jihar Filato sun kashe sabbin ma’aurata […]
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a jihar Filato sun kashe sabbin ma’aurata […]