‘Yan bindiga a Binuwai sun ƙona gidaje 23

0
37
'Yan bindiga a Binuwai sun ƙona gidaje 23

‘Yan bindiga a Binuwai sun ƙona gidaje 23

Daga Ali Sanni

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun ƙona gidaje 23 a yankin Egwuma da ke ƙaramar hukumar Agatu dake jihar Binuwai.

Mazauna yankin sun bayyana cewa mutane da dama sun tsallake rijiya da baya a harin wasu kuma da raunukan harbin bindiga.

Shugaban ƙaramar hukumar Gari, Philip Ebenyakwu, ya shaida wa manema labarai a Makurɗi, babban birnin jihar, cewa mutane uku ne suka tsira da raunukan harbi.

KU KUMA KARANTA: Mayaƙan ‘Boko Haram’ a Borno sun kashe ɗan sanda da ƙona motocin sintiri

Ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, kuma waɗanda aka ji wa raunukan suna samun kulawa a asibiti.

Ya ce, “Makiyaya ɗauke da makamai daga jihar Kogi suna yawan kai hare-hare a Agatu ta yamma.

“Yankin da aka kai wa hari yana iyaka da jahar Kogi, kuma yana yawan fuskantar barazana.

“Ranar lahadi makiyayan suka kai hari a yankin Egwuma, inda suka ƙona gidaje 23 suka sace babura biyu.”

Duk da haka, Ebenyakwu, ya yaba wa jami’an tsaron da aka tura yankin.

Ya bayyana cewa a ranar Asabar wani sojan ruwa ya ƙwace jirgin ruwa da ’yan bindiga ke shigowa a kai daga jihar Nasarawa.

Wakilinmu yayi ƙokarin tattaunawa da kakakin ‘yan sandar jihar ta Binuwai, SP Catherine Anene, amma hakan baiyuba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here