Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani ɗan jarida Usman Umar Sahabi a jihar Adamawa.
An sace ɗan jaridar ne a gidansa dake Wuro Chekke, Yola da sanyin safiyar Alhamis, 2 ga Nuwamba, 2023.
“Wasu ‘yan bindiga kusan biyar ne suka kai farmaki gidansa da misalin karfe 1:00 na safiyar yau, inda suka shiga ɗakinsa inda suka yi ta harbin bindiga, har ya zuwa yanzu ba a nemi kuɗin fansa ba,” inji wata majiya daga iyalan.
Sahabi ma’aikacin gidan rediyon ABC Yola ne kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Adamawa Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ‘yan sandan sun baza duk wani kadarorinsu na aiki don ganin an ceto ɗan jaridar da ransa.
KU KUMA KARANTA: An kashe iyalan ɗan jaridan Aljazeera a Gaza
“Mun tura jami’an mu na aiki tare da yin aiki ba dare ba rana don ganin an ceto dan jaridar da aka sace da rai,” in ji PPRO.
“Ba mu huta ba tun da muka samu labarin faruwar lamarin kuma muna tursasa masu laifin har sai mun ƙuɓutar da ɗan jaridar a raye tare da kama waɗanda suka aikata laifin.”