No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan banga sun hallaka wasu ’yan bindiga uku suka addabi yankin Ngaski da ke jihar Kebbi da satar mutane.

’Yan bindigar sun gamu da ajalinsu a hannun ’yan banga ne a maɓoyarsu da ke ƙaramar hukumar Ngaski ranar Alhamis.

Masu garkuwa da mutanen sun jima da addabar yankin kafin dubunsu ta cika bayan ’yan banga sun fara cafke masu yi musu leƙen asiri.

Darektan tsaro na jihar, AbdulRahman Usman ya ce “bayan kama masu yi wa ’yan bindigar leƙen asiri ne suka jagoranci ’yan banga zuwa maɓoyarsu da ke cikin jeji, inda aka yi musayar wuta da su,” suka ci ƙarfinsu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano

Ya bayyana jin daɗinsa bisa nasarar da ’yan bangar suka samu ba tare da asarar rai ko rauni ba.

Ya kuma jinjina musu game da yadda suke taimaka wa hukumomin tsaro wajen magance matsalar tsaro a jihar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...