‘Yan APC sun fara azumi bayan Abba ya garzaya kotun ƙoli

0
210

Daga Haruna Idi Hassan

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta buƙaci ɗaukacin mambobinta da ƴan kasuwar da suka yi asarar dukiyarsu sakamaƙon rushe musu shaguna da gidaje da gwamnatin jihar ta yi da su fara azumi a yau.

Shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas, a cikin wani saƙon murya ya buƙaci da su yi addu’a tuƙuru domin nuna godiya ga nasarar da jam’iyyarsu ta samu nasara a ƙotun dauƙaka ƙara a ranar Juma’a.

Saƙon nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP, ya yanke hukuncin ƙalubalantar hukuncin kotun dauƙaka ƙara a gaban kotun ƙoli.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya ce ya umarci lauyoyinsa da su ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke.

KU KUMA KARANTA: Saƙon Dr. Nasiru Gawuna ga al’ummar Kano bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Ya ƙara da cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa “Kotun ƙoli za ta sauke hukuncin da yardar Allah.”

Tun da fari kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta fara soke Abba, hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar daga bisani.

Hukunci biyu sun haifar da zazzafar muhawara musamman a tsakanin masu sharhi kan al’amuran siyasa a jihar.

Kazalika, hukuncin ya haifar da cece-ƙuce da fargaba a tsakanin mazauna jihar.

Leave a Reply