’Yan acaɓa sun kai hari ofishin ’yan sanda a Legas

0
87
’Yan acaɓa sun kai hari ofishin ’yan sanda a Legas

’Yan acaɓa sun kai hari ofishin ’yan sanda a Legas

Wasu ’yan acaba ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki ofishin ’yan sanda na yankin Ipaja da ke Jihar Legas a safiyar ranar Litinin.

Farmakin ya sa ’yan sandan yin artabu da ’yan acaɓar da suka kai hari ofishin.
Lamarin dai ya haifar da firgici da ruɗani a tsakanin mazauna yankin, lamarin da ya sa aka aike ƙarin jami’an ‘yan sanda don tabbatar da tsaro.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta shawo kan lamarin.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe mutum 12 a Kaduna, sun kai hari a ofishin ƴan sanda a Zamfara

“Jami’an ’yan sandan yankin Ipaja sun yi nasarar daƙile wani hari da wasu ‘yan acaɓa suka kai musu a safiyar yau.

“Harin na zuwa ne bayan da jami’an ’yan sanda suka hana yin sana’ar acaɓa a Jihar Legas.

“Maharan waɗanda suka yi dandazo, sun afka wa ofishin ‘yan sandan yankin da muggan makamai, inda suka yi ƙoƙarin ƙwace ofishin. Sai dai jami’an ofishin sun yi artabu da su, har zuwa lokacin da aike musu ƙarin tawaga.

“Biyu daga cikin maharan sun samu munanan raunuka yayin harin. An yi nasarar cafke wasu daga cikin maharan.

“Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da doka da oda a tsakanin al’umma,” in ji Hundeyin.

Leave a Reply