Daga Ibraheem El-Tafseer
Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun ba da sanarwar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Talata 3 ga watan Oktoba a faɗin ƙasar.
Ƙungiyoyin NLC da TUC sun bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da suka ƙira da yammacin ranar Talata a babban birnin ƙasar, Abuja.
Sun buƙaci rassansu na jihohi su harhaɗo kan ‘yan ƙwadago da sauran jama’a don gudanar da jerin zanga-zanga a faɗin Najeriya.
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya na cewa sun fahimci cewa shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon biyu sun warware bambance-bambancen da suka sanya ƙungiyar NLC shiga wani yajin aikin gargaɗi tsawon kwana biyu, ba tare da takwararsu ta TUC ba.
NLC ta ƙaurace wa aiki a ranakun 5 da kuma 6 ga watan Satumba da muke ciki don matsa lamba ga gwamnatin ƙasar a kan ta shawo kan wahalhalun da ‘yan Najeriya, musamman ma’aikata ke ciki, sakamakon cire tallafin man fetur.
KU KUMA KARANTA: Katsewar wutar lantarki sakamakon yajin aikin gargaɗin NLC – AEDC
A cewar sanarwar da sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja ya fitar, ƙungiyoyin na gudanar da taron ne ta intanet.
A lokaci guda kuma, ministan ƙwadago, Mista Simon Lalong ya roƙi shugabannin NLC su dakatar da shirinsu na tafiya yajin aikin, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati na nan a kan ƙudurin magance damuwar da suka bijiro da ita.
Ministan, kamar yadda tashar Channels TV ta ruwaito, ya kuma nunar da cewa ɗaya daga cikin manyan buƙatun NLC a taron da suka yi na baya, tuni an cimma ta, inda ta ba da umarnin sakin shugaban ƙungiyar ma’aikatan sufurin mota a ƙasar.