Daga Ibraheem El-Tafseer
Ƙungiyoyin ƙwadago sun gabatar da rubutaccen saƙo ga Majalisar Tarayyar Najeriya, a wani ɓangare na zanga-zangar da ta gudanar ranar Laraba.
‘Yan ƙwadagon sun buƙaci shiga tsakanin ‘yan majalisar a dambarwarsu da ɓangaren zartarwa ko kuma su tsunduma yajin aiki a faɗin ƙasar daga ranar Alhamis.
Sai dai mai tsawatarwa, Sanata Ali Ndume, wanda shi ne jagoran kwamitin da majalisar ta wakilta don karɓar masu zanga-zangar da suka je harabar majalisar a Abuja, ya roƙi ‘yan ƙwadagon a kan su jinkirta aniyarsu ta shiga yajin aiki daga Alhamis ɗin nan.
Ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon su bai wa Majalisar Tarayyar mako ɗaya a ƙoƙarinta na shiga tsakani don kawo ƙarshen wannan taƙaddama ba tare da durƙusar da harkokin gwamnati da na tattalin arziƙi a ƙasar ba.
KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta ayyana za’a shiga yajin aiki a watan Agusta a faɗin ƙasar
Tun da farko, masu zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin shugaban NLC babbar ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, Kwamared Joe Ajero sun yi wa majalisar tsinke cikin rakiyar jami’an tsaro, a yunƙurinsu na ganawa da masu yin dokar.
Sai dai sun gamu da turjiya da farko daga jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga karya ƙofar shiga harabar majalisar kuma dandazon masu zanga-zangar suka ɗunguma ciki.
Su dai, ‘yan ƙwadagon a cikin saƙon da suka gabatar wa majalisar sun jaddada buƙatun cewa ya zama wajibi a gyara matatun man fetur na Najeriya ciki har da na Warri da Kaduna.
Sun kuma ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa farashin man fetur yana tafiya ne daidai da hawa da sauƙar farashin dala a kasuwar duniya.
A cewar saƙon, ya zama wajibi gwamnati ta gaggauta aiwatar da alƙawurran da ta ɗauka na sauƙaƙa tsadar rayuwa.
Kuma sun nemi a sake mayar da tallafin man fetur da aka cire saboda a cewarsu babu ƙasar da ba ta tallafawa talakawanta a duniya.
[…] KU KUMA KARANTA: ‘Yan ƙwadago a Najeriya sun bai wa Majalisa wa’adi ko su shiga yajin aiki […]