Connect with us

Labarai

Yadda za ka kare kanka daga masu ƙwacen Whatsapp

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

A kwanan nan ƙwacen shafin sa da zumunta na WhatsApp, wanda a turance ake kira ‘Hacking’ ya zama ruwan dare, mafi yawan mutane sun rasa ta yaya hakan yake faruwa. To yanzu za mu ɗan yi bayanin yadda mutum zai kare kansa da faɗa wa tarkon waɗannan masu kutsen. Shi Whatsapp mutane daya wa suna mamaki, wasu mutanen ma gani suke kamar ba zai yi yu a ƙwace shi ba, saboda lambar waya kaɗai ake amfani da shi wajen buɗewa kuma mafi yawan mutane basu damu da yin hira ‘chatting’ da mutanen da ba su san su ba a WhatsApp ɗin.

Wasu har sukan iya cewa ma ta ina Bature zai samu lambar su har ya iya ƙwace musu WhatsApp? Shin ta yaya ma zai fara? Da dai wasu tunani da suka dogara da su na ƙin yarda ana iya ƙwacewa.

Duk da cewa yanzu an fara ganin zahiri cewa ana iya ‘Hacking’ ɗin WhatsApp ɗin, kuma wasu ma an musu, to wane mataki ya kamata a ɗauka dan ganin an daƙile faruwar hakan nan gaba?

Hanya mafi sauƙi da za ka bi don daƙile yi maka kutse a WhatsApp ɗinka shi ne, ka shiga ‘SETTING ‘ a cikin WhatsApp ɗin naka, sai ka shiga ‘TWO STEP VERIFICATION’ ka saka shi.

KU KUMA KARANTA: Yadda za ka kare shafinka na Facebook da Twitter daga masu ƙwace

Yaya ake saka ‘two step verification’ a WhatsApp?

Idan ka shiga ‘settings’ ka duba ‘account settings’ a ciki za ka ga ‘Two Step Verification’ sai ka shiga ka saka abin da suka tambaya, sannan kuma za su buƙaci ka saka Email ɗinka domin toshe duk wani yunƙuri na yi maka kutse a WhatsApp ɗinka.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like