Connect with us

Labarai

Yadda yaro ɗan shekara 9 ya yi garkuwa da ƴar shekara 5 a jihar Bauchi

Published

on

Kwamishiniyar harkokin mata da cigaban ƙananan yara, Hajara Gidado, ta bayyana yadda wani yaro Almajiri ɗan shekara tara, wanda aka ɓoye sunansa, ya sace wata yarinya ƴar shekara biyar a gidan mahaifinta. Legit Hausa ya wallafa.

Ta bayyana hakan ne a wajen buɗe taron horar da malaman Tsangaya da na Islamiyya na kwanaki biyu a ɗakin taro na Sa’ad Abubakar da ke Hajj Camp a Bauchi, cewar rahoton The Nation.

Yaron, a cewarta tun asali an kawo shi ne domin neman ilimin addinin Islama daga jihar Kano zuwa Magama Gumau da ke ƙaramar hukumar Toro.

Ta ce daga baya ya samu tsohuwar wayar Android ta hanyar barace-barace sannan ya fara koyon yadda a ke aikata miyagun laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, rahoton Tribune ya tabbatar.

A kalamanta:

“Wata rana yana cikin bara, ya isa wani gida, sai ya haɗu da wata yarinya ƴar shekara biyar, ya ɗauke ta ya kai ta wata makaranta a garin. Bayan wasu sa’o’i sai yarinyar ta ji yunwa, shi ma ya ji yunwa. Don haka sai ya zagaya domin neman abin da su biyun za su ci.”

“Ya yi ƙoƙarin samun lambar wayar mahaifin yarinyar, wanda ya daɗe yana neman yarinyar. Almajirin ya ƙira mahaifinta ya ce ya kawo naira miliyan biyar a matsayin kuɗin fansa. Mahaifin yarinyar yayi biris dashi.”

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Adamawa sun yi garkuwa da ɗan jarida

“Da yamma ya yanke shawarar mayar da yarinyar gidan da ya ɗauke ta. A hanya sai ya gamu da mahaifinta, ya tambaye shi inda ya samo yarinyar, sai ya shaida wa mahaifin cewa ya yi garkuwa da ita, kuma tun da mahaifin bai kawo kuɗin da ya nema ba, sai ya yanke shawarar mayar da ita.”

Ta ce mahaifansa da malamin da aka kawo shi domin yin karatun addini a wajensa, sun bar shi a gidan gyara hali na ƙananan yara na Bauchi, inda yake zaman gyaran hali bayan kotu ta yanke masa hukunci kan laifin da ya aikata shekara uku da suka gabata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like