Yadda ‘yan yahoo suka yi garkuwa da abokin ta’asarsu kan kuɗin damfara

2
473

A ranar Litinin, 26 ga watan Disamban 2022, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi ‘yan damfarar yanar gizo ne, waɗanda ake yiwa laƙabi da ‘yan yahoo, bisa laifin yin garkuwa da abokin aikinsu akan raba kuɗaɗen da suka samu harkarsu ta damfara da zamba cikin aminci.

Mai magana da yawu rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Neptune Prime Hausa cewa waɗanda ake zargin, Agbe Simeon da kuma wata mace mai suna Messiah Nicky sai Oladapo Dolapo da kuma Yetunde Shonola wacce ita ma mace ce, an kama su ne a ƙauyen Orile imo da ke ƙaramar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun, biyo bayan wani bayani da ‘yan sanda suka samu a garin.

KU KUMA KARANTA:Dubun wata mace da ta ƙware a garkuwa yara ta cika

‘Yan sandan da ke aiki a sashin Owode Egba, sun shaida cewa wani mutum mai suna Haruna Usman, wanda aka yi garkuwa da shi tun ranar Alhamis, 22 ga watan Disamban 2022, an yi garkuwa da shi a wani wuri a Orile Imo, bayan bayyanar labarin ne sai DPO na yankin Owode Egba, CSP Popoola Olasunkanmi, yayi gaggawar tattara mutanensa tare da kutsawa yankin, inda aka cafke huɗu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da Haruna Usman, yayin da wasu biyu suka tsere.

Kuma binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda aka yi garkuwa da shi da waɗanda ake zargin ‘yan ƙungiyar damfara ne ta yanar gizo, kuma a kwanan baya sun damfari wani wanda har yanzu ba a san sunan sa ba akan kuɗi naira miliyan ashirin da shida da ɗari huɗu da talatin da bakwai da ɗari tara da hamsin (N26,437,950). ), amma wanda abin ya shafa ya ba sauran abokan aikin sa Naira miliyan biyu da dubu ɗari biyu kawai, (N2,200,000) inda ya shaida masu cewa, ba a biya kuɗin gaba ɗaya ba.

Hakan ne ya fusata abokan harkallar tada inda daga nan suka kai shi wani gida da ke Orile Imo suka yi garkuwa da shi a can tun ranar Alhamis, 22 ga Disamba, 2022, tare da barazanar kashe shi a can idan ya ƙi ba su cikakken kasonsu.

Amma a lokacin da suke wajen, bayanai sun isa ga ‘yan sandan da suka shiga, inda suka ceto wanda aka yi garkuwa da shi, suka kuma cafke huɗu daga cikin waɗanda suka shirya garkuwar, yayin da wasu suka tsere.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin yaƙi da satar mutane na sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

2 COMMENTS

Leave a Reply