Yadda ‘yan sanda suka ceto ɗan jarida daga hannun masu garkuwa da mutane

1
329

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar 11 ga Maris, 2023, sun ceto wani ɗan jarida mai suna Oduneye Olusegun, wanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a unguwar Mobalufon da ke Ijebu Ode a ranar 9 ga watan Maris, 2023.

A wata sanarwa da Abimbola Oyeyemi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, ya sanyawa hannu, ya ce an yi garkuwa da ɗan jaridar wanda ya fito domin zuwa Abeokuta a unguwar Mobalufon a cikin motarsa ƙirar ​​Toyota Camry da misalin karfe 7:50 na yammacin ranar Alhamis 9 ga watan Maris, 2023.

Washegari da safe masu garkuwan suka ƙira matarsa ​​ta wayarsa inda suka buƙaci a basu naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa.

KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

“Bayan da kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Frank Mba ya sami labarin, sai ya umurci babban DPO na yansandan da ke aiki a unguwar Obalende ta jihar, SP Murphy Salami, wanda hurumin sa ne inda lamarin ya faru domin tabbatar da ceto ɗan jaridar.

“A bisa bin umarnin Kwamishinan, DPO ya tattara jami’ansa tare da gudanar da bincike bisa fasaha da kuma bayanan sirri kan lamarin, kuma ƙoƙarinsu ya cimma ruwa lokacin da aka gano motar ɗan jaridan, ƙirar Toyota Camry a unguwar Idimu da ke Legas, inda masu garkuwar suka tafi da shi, suna jiran kuɗin fansarsa.

“Da ganin ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun yi ta harbe-harbe inda ‘yan sandan suka mayar masu da martani, an kuma yi musayar wuta na kusan mintuna 45 kafin daga bisani suka bar motan suka ja da baya, bayan da suka samu raunuka daban-daban na harbin bindiga.

Abinbola Oyeyemi ya ƙara da cewa, ‘yan sandan sun gano motar ɗan jaridar tayi kacakaca da jinin masu garkuwa da mutane sakamakon raunukan harbin da suka samu.

“Bayan da suka fahimci cewa ‘yan sanda sun ci karfinsu, sai suka bar ɗan jarida suka yi takansu inda suka tsere da raunuka a jikinsu.”

Yace, kwamishinan ‘yan sandan, CP Frank Mba, wanda ya yabawa mutanensa kan yadda suke nuna hazaƙa wajen ceto ɗan jaridar, ya yi kira ga jama’a musamman asibitoci da masu maganin gargajiya da su sanar da ‘yan sanda idan sun ga wani da harbin bindiga ya zo neman magani wajensu.

Frank Mba ya kuma gargaɗi masu aikata laifuka da su kaurace wa jihar Ogun, saboda rundunar ta shirya tsaf domin kai farmakin a duk inda suke.

1 COMMENT

Leave a Reply