Yadda wani mutum ya fille kan matarsa, ya sare hannun ‘yarsa

Al’ummar yankin Kampala da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato sun shiga alhini a ranar talata bayan wani mutum da ake zargin ya kashe matar tasa ta hanyar amfani da gatari ya yanke mata kai ya kuma yanke hannun ‘yarsa.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da matar da ta bar mijinta bayan da ba a warware matsalar ba ta koma gida zata kwashe kayanta.

Wani mazaunin unguwar mai suna Sunday Yaks, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a ranar talata.

Yaks ya ce shi ma mutumin ya yi amfani da gatari ya datse hannun ɗiyarsa mai shekara shida, ya ce, “a yanzu haka al’ummar Kampala na cikin ɗimuwa saboda abin da mutumin ya yi wa matarsa ​​da ‘yarsa.

Na san mutumin ana kiransa Mista Chayi kuma sunan ‘yar tasa Jessica mai kimanin shekara shida.

“Mutumin ya kasance suna samun matsalar aure da matar kuma a ƙarshe ta bar auren tare da ƙaramar ‘yarta.

KU KUMA KARANTA:Ya kashe mijin ƙanwarsa bisa zarginsa da bin mata

“Amma, jiya da yamma, matar ta koma gidansu da ke Kampala tare da ɗiyarta don kwashe kayanta.

“Ba mu san abin da ya faru ba amma mutumin ya yi amfani da gatari ya yanke kan matar da hannun ‘yar.

“Abin takaici ne yayin da wasu ’yan unguwar da aka sanar da su suka garzaya gidan.

“An garzaya da mutanen biyu asibiti amma matar ta mutu a lokacin da take jinya” in ji shi.

Yaks ya ce, shiga tsakani da jami’an tsaro suka yi ne ya ceto mutumin daga cin zarafin da wasu fusatattun matasa suka so su yi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan sandan da aka tura wa al’umma sun kama mutumin da ya kashe matarsa ​​bayan samun labarin.

PPRO ya ce, “Mutumin yana hannunmu a yanzu, za kuma a gurfanar da shi a gaban kotu idan aka kammala bincike kan lamarin.”


Comments

One response to “Yadda wani mutum ya fille kan matarsa, ya sare hannun ‘yarsa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Yadda wani mutum ya fille kan matarsa, ya sare hannun ‘yarsa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *