Yadda Sumaila na NNPP ya kawo ƙarshen Kabiru Gaya na APC da ya shafe shekaru 16 a majalisar dattawa

0
302

Ɗan takarar jam’iyyar NNPP mai wakiltar mazaɓar Kano ta kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila, ya doke Sanata mai ci, Kabiru Gaya na jam’iyyar APC kuma ya jawo ƙarashen zamansa a majalisar dattawa inda ya shafe shekaru 16 ana damawa da shi.

Kawu Sumaila, wanda tsohon mai taimaka wa shugaba Buhari ne a majalisar dokoki, kuma tsohon ɗan majalisar wakilai, ya doke Kabiru Gaya.

Sakamakon ƙarshe da jami’in zaɓe na INEC, Farfesa Ibrahim Barde ya sanar da safiyar Litinin, Kawu Sumaila ya samu ƙuri’u 319,857 inda ya doke Kabiru Gaya wanda ya samu ƙuri’u 192,518 da Galadanci Murtal Bashir na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 14,880 yayin da ɗan takarar LP Umar Darki ya zo na huɗu da ƙuri’u 2,875.

KU KUMA KARANTA: Atiku ya lashe zaɓe a mazaɓar elRufa’i da ta Ahmed Lawan

Kabiru Gaya tsohon gwamnan ne a jihar Kano a shekarar 1992 kuma an zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai tun daga shekarar 2007.

Kawu Sumaila a nasa ɓangaren ya wakilci mazaɓar Takai/Sumaila a majalisar wakilai daga shekarun 2003-2015 kafin a naɗa shi a matsayin mai taimaka wa shugaba Buhari a majalisa a 2015.

Leave a Reply