Yadda na ga baƙar rana

0
125
Yadda na ga baƙar rana

 

Yadda na ga baƙar rana

Daga Ali Sanni

Abin da ya sa na ƙira wannan ranar da baƙar rana shi ne abin da ya faru da ni a wannan ranar abin da na saba ji a labaran rediyo ko na kalla a talabijin ko na karanta a jaridu.
Sai ga shi kwatsam ya faru da ni allokacin da ban taɓa tunanin zan fuskanci irin wannan abun rayuwata.

A ranar wata Lahadi 10 ga watan Satumba shekarar 2017 da yamma misalin ƙarfe huɗu da mintuna 45 na samu mahaifiyata a ɗakinta na ce mata ina so na je gidansu abokina da ke unguwar Ikotun da ke Legas.

Buɗar bakin mahaifiyata ta ce, Ali ka yi haƙuri yamma ta yi, unguwar da za ka je tana da nisa ga shi idan dare ya yi ba tsaro sosai komai na iya faruwa ka bari sai da safe mana.

Ni kam da kafiyar tsiya na ce wa Mama ai yau Lahadi ba cunkoso a hanya nan da awa biyu insha Allahu zan isa gidan nasu.

Sai Mama ta ce to Ali Allah ya tsare amma ka da ka tafi da sabuwar wayarka, ka tafi da tsohuwar, nan ma na ƙi ɗaukar shawarar datijuwar nan.

Ina ji da sabuwar wayata ta dubu ɗari ‘Samsung’ ƙirar Galaxy J 7 wadda ranar juma’a na sayeta.

Haka na taho da wayata da kayan sawata guda da takalmina shima sabo na dubu biyar.

KU KUMA KARANTA:Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Munata tafiya salin alun har nazo inda zan hau motar ƙarshe wacce zata ajiye ni a layin gidan su abokina kawai zai naga an nunani da bindiga ance na miƙo wayata wacce tunda na shiga cikin motar naketa buga wasanin da itta cikin nishaɗi.

Bansan lokacin da na mika wayarba jikina na rawa bakina ya kasa cewa uffan.

Suka ƙwace jakata suka buɗe suka ɗauki sabon takalmina suka miƙo mun jakar.

Haka na kasance cikin dimuwa bansan lokacin da na fita daga motar ba sai ji nayi wata mata tana cewa wayyo dubu dari biyar dina chan naji wata budurwa ittama tana kururuwar cewa wayyo kuɗin makarantata.

Adaidai wannan lokacin na gane ashe rashin sani motar ɓarayi muka hau.

Sai kawai naji hawayen bakin ciki na zuba daga idanuwa na, ayayin da nake tuna shawarwarin da mahaifiyata ta bani naki dauka.

Nan take na tuna da kalmar da Bahaushe ke cewa danasani keyace.

Saiko na miƙe ganin tawa asarar mai sauki ce tunda waya ta dubu ɗari da takalmina na dubu biyar aka kwace.

Saina juya hanyar komawa gida na fasa ƙarasawa gidansu abokin nawa.

Nidai nasan dare yayi sosai amma banida agogo ko waya dazan duba lokaci, saboda a lokacin hankalina baya jikina burina kawai na ganni agida.

Aikuwa dake Legas gari ne da ake yawo ba dare ba rana gashi daddare ne cikin dan ƙanƙannin lokaci na karaso gida.

Ina zuwa gida na fara buga kofa saboda nasan kowa yayi bacci.

Allah sarki uwata ashe batayi bacci ba sakamakon ta ƙira wayata taji akashe ni kuma ban ƙirata ba.

Kafin mai gadi yazo ya buɗe mun kofa sai naji muryarta daga sama tana cewa Ali lafiya?

Sai kawai hawayen da ya riga ya taru a iddo na ya fara zubowa hawayen bakin ciki da nadama.

Ina shiga falo ta rungumai ni tace ya akayi ɗana? Nace mama wallahi na hau motar ɓarayi sun ƙwace mun waya da takalmina.

Mai makon tayi faɗa sai tace kayi haƙuri ƙaddara ce, basu jima ciwo ba daiko? Na gyaɗa kaina tace toh nagode wa Allah.

Tace dani kayi haƙuri gobe zan siyama irrin wayar da takalmin naka kaje kayi wanka kazo kaci wani abu kafin ka kwanta.

Allah sarki uwata sai naji daɗi na kama hawayen farin ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here