Yadda mota ta faɗo daga saman gada a Abuja (Hotuna)

Hatsari ya rutsa wani mutum da abokinsa yayin da motarsu ta faɗo daga saman gadar shatale-shatalen Berger da ke Abuja.

Neptune Hausa ta ruwaito lamarin ya faru a ranar Alhamis, yayin da motar kirar Toyota Camry ta faɗo daga kan gadar da misalin ƙarfe 3:10 na rana.

Motar mai lamba ABJ 135 HF, ta fito ne daga yankin Area 1 ne, yayin da ɗaya daga cikin tayoyin motar ta fashe, lamarin da ya kai ƙwace wa direban tare da fadowa daga saman gadar.

Wani ganau ya tabbatar da faruwar lamarin.

KU KUMA KARANTA: Mutum 6 sun rasu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Ebonyi

“Ina tare da abokina sai ga mota ta faɗo daga kan gadar, tare da taimakon sauran mutanen da ke kusa, mun samu nasarar ƙuɓutar da su tare da kai su asibiti.”

Ga hotunan motar a nan:


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *