Yadda magidanci ya ƙone matarsa da fetir saboda abinci

1
449

Wani mutum mai shekara 46 mai suna Hassan Azeez ya shiga hannun jami’an ‘yan sandan jihar Ogun, bisa laifin zubawa matarsa ​​fetur da kuma cinna mata wuta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya sanyawa hannu, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da mahaifin matar, ya shigar a sashin rundunar da ke Ibogun, wanda ya bayar da rahoton a ranar 22 ga watan Oktoban 2022, cewa mijin nata ne ya kona ɗiyarsa Olayinka Hassan saboda wani rashin jituwa a tsakanin su,ya ce an garzaya da ɗiyar tasa mai ɗa guda asibiti a da ke garin Ibadan inda ake kula da lafiyarta.

KU KUMA KARANTA:Yadda wani mutum ya kashe matar sa saboda burodi

“Bayan rahoton, DPO reshen Ibogun, CSP Samuel Oladele ya yi gaggawar tattara mutanensa suka nufi wurin, amma kafin su isa wurin, wanda ake zargin ya tsere.

“Tun daga lokacin ne jami’an ‘yan sanda ke bin sahunsa har zuwa ranar 22 ga watan Janairu inda a ƙarshe aka kama shi.

“Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi ikirarin ya gudu zuwa jamhuriyar Benin ya kuma amsa laifinsa, amma ya ɗora laifin a kan shaiɗan.

Hassan Azeez, wanda ake zargi

“A cewarsa, ya bukaci matar tasa ta shirya masa abinci, amma maimakon ta shirya masa abincin, sai ta shagaltu da yin wanki.

“Ya ci gaba da cewa ya fusata ne saboda yunwar da yake ji, abun da ya sa shi zuba mata man fetur ya banka mata wuta.

“Lokacin da aka tambaye shi kayan wa matar ke wankewa a lokacin, sai ya amsa da cewa kayan sa ne” Oyeyemi ya ce .

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na ‘yan sanda a jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

1 COMMENT

Leave a Reply