No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wata mata, mai suna Amina Guguwa mai shekara 50 da haihuwa bisa zargin kashe uwargidanta mai suna Amina Koli mai shekaru 60 a duniya.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Ahmad Mohammed Wakil, a wata sanarwa, ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Miya da ke karamar hukumar Ganjuwa a jihar.

Bayanin da rundunar ‘yan sandan ta samu, ya nuna cewa a ranar 1 ga watan Junairun 2023, matar ta shaƙe abkiyar zaman aurenta ta har lahira sakamakon wata arangama da suka yi a tsakaninsu.

Wakil ya ce wanda ake zargin, kamar yadda rahoton ya bayyana, ta yi amfani da ƙarfi wajen shake wuyan marigayiyar da karfi, wanda a sakamakon haka ta mutu nan take.

KU KUMA KARANTA:Yadda matashi ya kashe kishiyar uwarsa da ƙanwarsa a Kano

SP Wakil ya ci gaba da cewa, “Da samun rahoton ne aka tura tawagar jami’an tsaro, inda suka garzaya wurin da lamarin ya faru, suka kwashe wanda aka kashe zuwa babban asibitin Ganjuwa domin a duba lafiyarta.

“Wani likita ne ya tabbatar da cewa ta mutu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike, bayan haka kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...