Yadda likitoci suka koma yin tiyata a barandar asibitoci saboda rashin ɗakuna a Gaza

0
202

Asibitoci sun yi gargaɗin cewa mutane da dama za su rasu saboda rashin kayan aiki.

A lokacin da Asibitin Indonesia na Gaza yake samu ƙaruwar majinyata da suka samu munanan raunuka a dalilin hare-haren bama-baman Isra’ila, likitoci sun koma shirya wani ɗan wajen yin tiyata a barandar asibitin saboda asalin ɗakunan tiyatar sun cika, in ji su.

Saboda yadda ƙarancin magunguna da rashin wutar lantarki da hare-haren bama-bamai suke shafar asibitoci, dole likitoci a Gaza suka koma aiki ba dare ba rana domin kula da majinyatan da ake kawo musu kusan a kowane lokaci.

“Muna yin awa ɗaya-ɗaya ne saboda ana iya kawo mana waɗanda suka samu rauni a kowane lokaci.

“A lokuta da dama mukan yi tiyata a baranda, ko kuma a ɗakunan zaman masu kula da majinyata,” in ji Dakta Mohammed al Run.

Ya yi wannan jawabin ne jim kaɗan bayan harin bam ya bugi wani sashe a Asibitin Indonesia, wanda yake kusa da hanyar da sojojin Isra’ila ke ƙara ƙaimin kutsawa domin shiga yankin na Falasɗinu mai ɗimbim mutane, da kuma yadda suke ganin alamar man fetur ɗinsu ya kusa ƙarewa kamar yadda likitocin suka bayyana.

KU KUMA KARANTA: An kashe ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya 64 a Gaza

Tankokin Isra’ila sun shiga Gaza, mazaunin mutum miliyan 2.3 bayan kimanin mako uku suna jefa bama-bamai a yankin saboda mayar da martani a kan harin mayaƙan Hamas na ranar 7 ga Oktoba inda suka yi awon gaba da mutum 240 ’yan Isra’ila.

Ma’aikatan lafiya a yankin wanda ke ƙarƙashin Hamas sun ce an kashe sama da mutum 8,500 a hare-haren na Isra’ila a Gaza, ciki har da ƙananan yara 3,500.

A Arewacin Gaza, inda Isra’ila ta umarci miliyoyin mutane su bar gidajensu su koma kudancin yankin, samun kiwon lafiya na cikin abubuwa da suka fi wahalar gaske.

Leave a Reply