Connect with us

Zaɓen 2023

Yadda jam’iyyar PDP ta kwace kujerar gwamna a Zamfara

Published

on

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara na jam’iyyar APC ya sha kaye a zaɓen bayan ya sake tsayawa takara a hanun Lawal Dare na jam’iyyar PDP.

Jami’in zaɓe Farfesa Kasimu Shehu ya ce Dare ya samu ƙuri’u 377,726 inda ya kayar da gwamna Bello Mohammed Matawalle wanda ya samu ƙuri’u 311,976.

Matawalle yayi ta fafutukar ganin ya sake samun nasara bayan an bayyana akasarin gwamnoni 11 da suka nemi tazarce suka yi nasara amma a ƙarshe haƙarsa bata cimma ruwa ba.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai ya ba da gudumawar shanu 59 a mazaɓarsa a Zamfara | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Kotu

Kotu ta soke zaɓen Gwamna Lawan na Zamfara

Published

on

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta a ranar Alhamis ta soke nasarar Da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya samu.

A sakamakon haka, kotun ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

Kotun dai ta ce za a sake zaɓen ne a wasu ƙananan hukumomin Jihar guda uku.

Ƙananan Hukumomin su ne Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukyun.

A cewar kotun, hukuncin da Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Gwamnan ya yi a baya, wanda ya tabbatar da nasarar Dauda, bai yi la’akari da hujjar da jam’iyyar APC mai ƙara ta gabatar ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Lawan ya amince da naira biliyan huɗu don gyara hanyoyi a Gusau

Kazalika, kotun ta yi fatali da sakamakon da APC da kuma Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta bayar a ƙaramar Hukumar Maradun.

Tsohon Gwamnan Jihar, kuma ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle ne dai ya shigar da ƙarar yana neman a soke nasarar Dauda a zaɓen.

Hukumar INEC dai ta bayyana Dauda Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.

Continue Reading

INEC

INEC ta bayyana Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaɓen Imo

Published

on

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta bayyana Gwamna Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Imo da aka gudanar a jiya Asabar.

Abayomi Sunday ,jami’in hukumar zaɓe ta INEC daga cibiyar tattara sakamakon zaɓen jihar dake Owerri, ne ya bayyana wanda ya lashe zaɓen a safiyar yau Lahadi.

Hope Odidika Uzodinma ɗan takarar APC ya samu ƙuri’u 540,308 inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, wanda ya samu ƙuri’u 71,503 yayin da ɗan takarar jam’iyyar Labour, Athan Achonu, ya zo na uku da ƙuri’u 64,081.

KU KUMA KARANTA: Matasa a Imo sun kama ɗan sanda bisa zargin sace ƙuri’un zaɓe

Hukumar zaɓen Najeriya ganin cewa Hope Odidika Uzodinma ya cika dukkan ka’idojin a ɓangaren da ya shafi doka,banda haka ya kuma samu rinjayen ƙuri’un da suka dace, an ayyana shi a matsayin wanda aka zaɓa.

Continue Reading

Labarai

Matasa a Imo sun kama ɗan sanda bisa zargin sace ƙuri’un zaɓe

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗi a zaɓen da aka yi wa ɗaya daga cikin jami’anta a jihar Imo.

Bidiyon wani jami’in da wasu matasa ke riƙe da shi da suka zarge shi da sace ƙuri’a a cibiyar tattara ƙuri’u ta Amakohia Ikeduru a lokacin zaɓen gwamna da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Da yake mayar da martani ga faifan bidiyon, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce;

‘’Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta na sane da zargin da ake yi wa wannan ɗan sanda da ake zargin yana da hannu wajen sace ƙuri’u a cibiyar tattara ƙuri’u ta Amakohia Ikeduru da ke jihar Imo. 

KU KUMA KARANTA: ’Yan daba sun buɗe wa masu zaɓe wuta a Bayelsa

Ba mu ɗauki wannan batu da wasa ba domin yana damun sahihancin rundunar da kuma yadda mambobinta za su iya tabbatar da ingancin zaɓe. 

Don haka muna tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da cikakken bincike, kuma za mu yi muku bayani nan da nan.  Yana buƙatar cikakken bincike.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like