Yadda fursunoni 3 suka tsere daga gidan yari

0
175

Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali na Ijebu Ode da ke ƙaramar hukumar Ijebu Ode a Jihar Ogun.

Fursunonin da suka tsere sun haɗa da wani ɗan fashi da makami da kisan kai, da wani wanda aka yanke wa hukuncin kisa sai wani wanda aka ɗaure kan laifin fyaɗe.

Kakakin ’yan sandan jihar, Victor Oyeleke, ya tabbatar wa Aminiya ranar Talata cewa, “Lamarin ya faru ne ranar Asabar da misalin karfe uku na safe.

“An tayar da wata tawagar jami’an tsaro dom gano inda suka shiga. Za mu yi aiki da sauran jami’an tsaro don sake kamo su.”

KU KUMA KARANTA: An yi wa fursunoni 72 afuwa a gidajen yarin Zariya

Rundunar So-Safe Corps reshen Ijebu Imushin ta fitar, ta sanar cewa “fursunoni uku da suka tsere daga gidan yari na Ijebu-Ode su ne: Hammed Adeboyejo, Fatai Taiwo Akande da Oguntona Aliu, duk wanda kuka gani cikinsu, ku gaggauta tuntuɓar ofishin So-Safe Corps da ke kusa da ku.”

Leave a Reply