Yadda Emefiele ya mallaki bankuna 3 ta ɓarauniyar hanya

An bankaɗo yadda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya saye bankunan Union, Keystone da Polaris ta ɓarauniyar hanya.

Wani rahoto da mai bincike na musamman da shugaba Bola ya naɗa, Jim Obazee ya tona yadda Emefiele ya mallaki bankin Keystone da bankin Polaris ba tare da biyan ko sisi ba.

Rahoto ya bayyana yadda wani aminin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, marigayi Alhaji Ismaila Isa Funtua da Emefiele suka saye bankuna biyu ba tare da biyan ko sisi ba.

A cewar rahoton da Jim Obazee ya miƙa wa Shugaba Tinubu a ranar 20 ga Disamba, Emefiele ne ya saye bankunan Union.

Aminiya ta samu waɗannan bayanai ne daga wasu takardu daga majiya mai tushe, amma har yanzu ba a bayyana sakamakon binciken a ga jama’a a hukumance ba.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta tsare Emefiele bayan DSS ta sake shi

Amma gwamnatin tarayya ta ce za ta ƙwace bankunan biyu da Emefiele ya saya a kan farashi mai rangwame.

“Mun kammala bincike kan wannan ciniki kuma muna dab da dawo da waɗannan bankuna biyu ga gwamnatin tarayya,” in ji rahoton.

An dakatar da Emefiele ne kwanaki kaɗan bayan hawan Tinubu kan karagar mulki.

Jim kaɗan da sallamar sa ne jami’an tsaro suka kama shi tare da tsare shi bisa zargin sa da laifin zamba.

Daga bisani shugaban ƙasan ya umarce su da hukumomin yaƙi da rashawa su binciki ayyukan CBN a ƙarƙashin jaogarcin Emefiele.

A ranar Asabar aka sako Emefiele daga gidan yari bayan ya cika sharuɗɗan beli ciki har da biyan naira miliyan 300.

Lauyoyinsa sun ƙi cewa komai game da badaƙalar sayar da bankunan.

Hakazalika mai magana da yawun gwamnati bai amsa bukatarmu ta neman ƙarin bayani ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *