Yadda biri ya fasa cikin yaro ɗan shekara 10 da kumbar yatsarsa ya ciro hanjinsa

0
220

Wani biri ya kashe wani yaro ɗan shekara 10 a ƙasar Indiya bayan ya yaga hanjinsa.

‘Yan sanda sun ce yaron mai suna Dipak Thakor, wasu gungun birai ne suka kashe shi a lokacin da shi da abokansa ke wasa a kusa da wani gidan ibada a Salki, wani ƙaramin ƙauye da ke yammacin jihar Gujarat, a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba.

 A cewar Mail Online, wasu gungun birai sun kai masa hari tare da abokansa, kafin ɗaya daga cikin dabbobin ya caka masa kumbar yatsarsa a cikinsa sakamakon haka hanjin yaron suka fito.

 An garzaya da yaron asibiti amma abin takaici ya rasu kafin likitoci su yi masa magani.

KU KUMA KARANTA: Mutumin da ya auri kada, ya ce zai riƙe ta cikin aminci babu cutarwa

 ‘Hanjin sa ya fito a harin.  An garzaya da shi zuwa gidansu, daga bisani aka kai shi asibiti inda likitoci suka tabbatar da cewa ya mutu a lokacin da aka isa da shi asibiti,’ kamar yadda wani jami’i ya shaida wa kafar yaɗa labaran ƙasar.

 Jami’in ya ƙara da cewa wannan shi ne hari na uku da gungun birai suka kai a cikin wannan mako kadai.

 Jami’in gandun daji Vishal Chaudhary ya ce shi da tawagarsa sun jima suna ƙoƙarin kama dabbobin masu haɗari.

Leave a Reply