Yadda babban taron APC na ƙasa ya gudana a Abuja

0
11
Yadda babban taron APC na ƙasa ya gudana a Abuja

Yadda babban taron APC na ƙasa ya gudana a Abuja

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sha yabo da caccaka a yayin da ya jagoranci taron majalisar ƙoli na jam’iyyarsa ta APC.

Bai zama abin mamaki ba yadda masu ruwa da tsaki a taron jam’iyyar suka kada kuri’ar nuna gamsuwa ga salon mulkin Tinubu da ya fara jawabi bayan hawa karaga da cire tallafin man fetur a Mayun 2023.

APC dai wacce hadakar jam’iyyu ce ta narke kuma ta hau karagar mulki a 2015, ta kawo karshen mulkin PDP na shekaru 16 duk da wasu daga jiga-jigan jam’iyyar tsoffin ‘yan PDP ne da ya sa wasu masu sharhi ke cewa babban canji a zahiri shi ne na alamun jam’iyya amma ba wani sauyin manufa ba.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin da ke sahun gaba a taron ya nuna kwarin gwiwar Tinubu zai yi mulki wa’adi biyu na shekara 8 “in Allah ya yarda shi zai sake cin zabe nan gaba, saboda ka san shi lamari idan kana da yanayi marar kyau ko rashin lafiya ka ke yi idan ka sha magani nan take sai ka ji wani abu marar dadi daga bisani kuma sannan a warke”

Taron dai ya gudana ba tare da halartar wasu jiga-jigan jam’iyyar ba da su ka hada da tsohon shugaba Muhammadu Buhari da kuma tsohon gwamnan Kaduna Nasir Elrufai da kalamansa ke nuna ya na adawa da lamuran jam’iyyar da ma gwamnatin Tinubu.

KU KUMA KARANTA:An kammala shirin taron ‘Qur’an Convention’ a Abuja

Masanin kimiyyar kididdiga Farfesa Sadik Umar ya nuna mamakin yadda taron ya tashi ba tare da jan hankalin shugaban kan halin da kasa ke ciki na kuncin tattalin arziki ba “ shekara biyu fa sun gagara su kira taro don su ce ga wani abu sai da ma El- rRufai ya goranta musu.”

Matasa masu kamfen din jam’iyyar sun bukaci kawo sauyin gaggawa don gudun kar a samu tangarda a kamfen din tazarce na nan gaba.

Garba A. Koma Gona na daga wadanda suka yi wa jam’iyyar kamfen a zaben 2023 “su na mantawa ne laifin da PDP ta yi a loakcin Jonathan bai kama kafar/farcen wannan ba amma yaya a ka yi tallar jam’iyyar PDP”

Daga dawowa dimokradiyya a 1999 PDP ta fara mulki inda ‘yan adawa su ka karba don haka duk bangarorin biyun sun hau karaga, yanzu kuma a na neman kulla wata tafiyar ta shinkafa da wake ko za a iya samun sabon lale ko kuwa a’a.

Leave a Reply