Al’ummar jami’ar Jos, sun shiga cikin tashin hankali biyo bayan kisan da wasu da ake zargin masu kisa ne, suka yi wa wata ɗaliba Level 400, a Sashen turanci.
Matar da aka kashe mai suna Ruth Yakadi, ‘yar kabilar Anaguta a jihar Filato, an kashe ta ne bayan wasu mahara suka yi mata fyade, inda bidiyon kisan ta, ya yi ta yaɗuwa.
Da aka tuntuɓi shugaban sashen turanci na jami’ar Jos, Farfesa Jeff Doki, ya ce marigayiyar ɗaliba ce wanda ta gama, tana jiran yin bautar ƙasa, bayan ta kammala karatu.
“Na rasa ɗalibai uku tun lokacin da na zama HOD a shekarar 2021, maza biyu a watan Yuli da Satumbar bana, 2022, a lokacin yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i” in ji shi.
KU KUMA KARANTA:Yadda wani mutum yayi wa Yaro fyaɗe har ya mutu
HOD ya umurci sauran malamai da su bayar da bayanai a rukunin WhatsApp na sashen.
Ya ce, “bayanan da suka zo min sun nuna cewa, yarinyar da aka kashe a daren ranar asabar da ta gabata, a farin gada,ɗaliba ce a sashen mu.
Dokta Douglas Kaze ne ke kula da ita kuma tana da matsala game da karatu ta, watakila ta kammala,ko bata kammala ba.
“Ina rokon Dr Kaze da Mrs Vera Aaron da Mista Innocent Dajang da su ba da bayanai game da ita a wannan shafin, don Allah. Sunanta Ruth Yakadi.l, ‘yar ƙabilar Anaguta ce..
“Bayanan da aka samu sun nuna cewa an yi wa yarinyar fyade, tare da kashe ta. Kamar yadda al’amura ke tafiya yanzu, muna tunanin ko masu fyade ne ko kuma masu kisan kai ne.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alfred Alabo, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna sane da lamarin kuma suna kan bincike.
[…] KU KUMA KARANTA:Yadda aka yiwa ɗalibar jami’a fyaɗe, aka hallaka ta […]