Yadda aka yi garkuwa da jami’an INEC a hanyarsu ta zuwa cibiyar tattara sakamakon zaɓe

1
433

An yi garkuwa da jami’in zaɓe na gwamnan jihar Zamfara a ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar, wacce ita ce mahaifar Gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle, wanda ya sake tsayawa takara don neman zama gwamna a karo na biyu.

Jami’an sun nufi hedikwatar hukumar zaɓe mai zaman kanta da ke Gusau, babban birnin jihar domin kai sakamakon zaɓen gwamnan na ƙaramar hukumar Maradun, inda aka yi garkuwa da su aka kuma kai su wani wuri da ba a bayyana ba.

KU KUMA KARANTA: Yadda ‘yan sanda suka ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar INEC na jihar, Muktari Janyau ya shaida wa manema labarai cewa an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Janyau ya ce, “Kwamishanan zaɓe na jihar Zamfara, Farfesa Sa,idu Babura Ahmed ya kai rahoton lamarin ga kwamishinan ‘yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace.”

A halin da ake ciki kuma, an bayyana sakamakon zaɓen a ƙananan hukumomi 9 cikin 14, kuma jam’iyyar adawa ta PDP ce ke kan gaba a ƙananan hukumomi bakwai.

1 COMMENT

Leave a Reply