Yadda aka toshe ruwan Alau Dam na Maiduguri – Maryam Abacha

0
168
Yadda aka toshe ruwan Alau Dam na Maiduguri - Maryam Abacha

Yadda aka toshe ruwan Alau Dam na Maiduguri – Maryam Abacha

Daga Ibraheem El-Tafseer

Uwargidan tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Hajiya Maryam Sani Abacha, a cikin wani faifayin bidiyo mai minti uku da ta yi, ta jajanta wa al’ummar Maiduguri, sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta auku a jihar.

Hajiya Maryam ta ce “ina jajanta wa al’ummar Najeriya da jihar Borno bisa ga ambaliyar ruwa da ta auku a jihar. Ni ‘yar asalin Maiduguri ce. Iyaye na duk daga jihar Borno suke. Ina yawan waya da dangin Mamana, ko da safiyar yau ma mun yi dasu, ana maganar za a canza musu muhalli, saboda unguwarsu ruwa ya cinye. Sannan muna haɗa tallafi na kuɗi da abinci za mu aika musu.

Tun a lokacin mai gida (Janaral Sani Abacha) ma an yi irin wannan ambaliyar ruwa kuma ya ba da taimako, yau kusan shekaru 30 kenan. To abin dai ga shi nan Allah ya aiko, ba yadda za a yi, Allah ya kiyaye na gaba.

Ya kamata a yi ƙoƙari a gyara wannan Dam ɗin, saboda kar ya sake auku wa a gaba. Mu ƙasar nan gaskiya muna da sakaci, kuma muna da ƙunci. Akwai lokacin da a ƙauyenmu Jere, ana yin noman shinkafa, to sai na ɗauki shinkafa na kawowa gwamnati ta gani, saboda a bunƙasa noman shinkafa. Tun da muna da shinkafa a ƙasar, kuma idan aka bunƙasa noman zai yiwu.

READ ALSO: Gwamnatin Kano za ta gina gidaje kyauta ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa

Unfortunate, wani ɗan gwamnati sai ya je ya sa aka toshe ruwan nan da yake zuwa daga Alau Dam ɗin, wanda ake noman shinkafar da shi. Kogi ne fa ƙarami, wanda ruwan yake zuwa ciki, bai kai Chalawa ba ma.

Ina faɗar haka ne saboda hali irin na mutanen mu, wanda bai kamata a yi haka ba.

Ai kuwa sai wani ɗan garin mu ya zo, sai nake ce masa kai kuma ko ɗanyar shinkafa ba za ka kawo mana ba, mu yi masa ko kunu. Sai ya ce ah! Ba ki san an toshe ruwan ba? Sai ya ce ai tuni an toshe ruwan. Sai na yi tunani na ce, ashe shinkafar nan da na kai wa gwamnati, ga abin da ta janyo.

To da mai gida (Abacha) ya zama shugaban ƙasa, sai na je na ƙira Gwamna, na ce masa akwai Dam da aka toshe, maza ka je ka buɗe. Wallahi kuwa da ya je, da gaske toshe ruwan aka yi. Da aka buɗe ga shi har yanzu ana amfani da shi, ana ta noman shinkafa.

To irin abubuwan da muke yi wa junan mu kenan, da yake mayar da mu baya. Duk abin da za a taimaki al’umma, don Allah, don Annabi a dinga taimako. A daina irin wannan Hassada da baƙin ciki.

Ka ga shi wannan ruwa da ya shigo, ya yi wa jama’a da yawa ɓarna, ga mutuwa. Ɓarna da ruwa ya yi ɗin nan na abinci a kasuwanni, kamar Suga da Gishiri, ka ga duk sun narke. Hatsi duk sun jiƙe, to ina mutane za su samu abinci su ci? Ga gida cike yake fal da ruwa, babu inda za a saka murhu. Allah ya kiyaye gaba.

Allah ya sa ruwa ne, ruwa kuma alheri ne. To an gode wa Allah tun da ba wuta ba ne. Ruwa rahama ne, Allah ya sa ya wanke zunubansu da kura-kuransu. Allah ya sa ya wanke wannan jini da Boko Haram suka zubar a Maiduguri. Kuma ina ƙira ga al’umma don Allah a kaiwa mutanen Maiduguri gudumawa, komai kaɗan ɗinsa.

Leave a Reply