Yadda aka karrama mai KEKE-NAPEP da ya dawo da miliyan 9 da ya tsinta a babur ɗinsa a Yobe

0
177

Ƙungiyar manyan sakatarorin jihar Yobe ta karrama Malam Ali Bulama, wani mai mai haya da Keke-NAPEP da ya mayar da naira miliyan tara da wani fasinjan da ya manta a cikin babur ɗinsa.

Da yake miƙa wa Bulama, mazaunin garin Jumban a ƙaramar hukumar Tarmuwa, takardar shaidar karramawa da kyautar tsabar kuɗi N100,000, shugaban ƙungiyar, Alhaji Maisandan Lawan, ya yaba wa mai Keke Napep ɗin bisa gaskiya da tsoron Allah da ya nuna.

“Wannan mutumin ya cancanci a san shi tare da karrama shi bisa yadda ya nuna gaskiya da sanin ya kamata don zama misali ga al’umma.

“Duk da cewar da ya so zai iya mallake waɗannan kuɗaɗe da ya tsinta, amma saboda gaskiyarsa da tsoron Allah da malamin ke da shi, sai ya yanke shawarar yin abin da ya dace ta hanyar mayar wa mai shi,” inji shi.

Maisanda ya yi ƙira ga Gwamnatin Jihar Yobe da masu hannu da shuni da su mara wa Bulama baya a kan gaskiya tare da bin sahun abin da suka yi na karrama shi.

KU KUMA KARANTA: Matuƙin Keke Napep ya mayar da miliyan 15 da wani fasinja ya manta a mashin ɗinsa

Ya kuma buƙaci jama’a musamman matasa da su yi koyi da Bulama ta hanyar nuna gaskiya da rikon amana a duk inda suka samu kansu.

A nasa jawabin, Bulama ya ce, mai kuɗin kuma mazaunin Maiduguri ya hau babur ɗinsa ne a Jumbam da misalin karfe 9:30 na daren ranar 17 ga watan Nuwamba.

“Da misalin karfe 11:30 ne bayan na kai gida, sai na ga wani buhu ɗauke da wasu kayayyaki da suka rage a babur ɗin.

“Lokacin da na gano cewa buhun yana ɗauke da wasu kuɗi, sai na yi gaggawar fita don neman mai shi, wanda kafin wani lokaci tuni labarin tsintuwar waɗannan kuɗaɗe ya bazu a wannan ƙauye namu na jumbam.”

“Bayan wani lokaci da taimakon wasu mutanen yankin, an gano mai kuɗin, inda na miƙa masa kuɗinsa.” inji shi.

Bulama, wanda babur din da yake amfani da shi ba nasa ba ne, hayarsa aka ba shi in yayi aiki ya kai balas ga mai shi, ya ce mai kuɗin ya ba shi N20,000 a matsayin nuna godiya.

Wannan  taron dai  ya samu halartar shuwagabannin al’umma da kuma jagororin masu amfani da keke-Napep na ƙaramar hukumar.

Leave a Reply