Yadda aka kama Ɗan Bello da sake shi a filin jirgin sama na Kano

0
340
Yadda aka kama Ɗan Bello da sake shi a filin jirgin sama na Kano
Bello Habib Galadanci (Ɗan Bello)

Yadda aka kama Ɗan Bello da sake shi a filin jirgin sama na Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jami’an tsaro sun kama shahararren ɗan gwagwarmayar shugabanci na gaskiya a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, bayan isowarsa Nijeriya a yau Asabar a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano.

Ganau sun ce wani rukuni na jami’an tsaro ne su ka yi wa Dan Bello tara-tara sannan su ka tafi da shi.

LEADERSHIP ta rawaito cewa sai dai bayan ƴan mintuna a tsare, sai aka sako Dan Bello, wanda ke zaune a kasar China, kuma kwai yanzu babu wani bayani da hukumomin tsaro kan dalilin kama shi.

KU KUMA KARANTA: An samu damar kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano – Ɗan Jarida Jaafar Jaafar

Daga bisani, wani lauya sananne kuma aboki na kusa ga Dan Bello, Abba Hikima, ya saka hotonsa tare da Dan Bello a shafinsa na Facebook da rubutun “Guys, we’re good!” wanda ke nuni da cewa an sako shi.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Dan Bello ya yi shura wajen fallasa aiyukan badakala da almundahana da masu riƙe da madafun iko ke yi a Nijeriya.

Leave a Reply