Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wata mata mai shekaru 53 da haihuwa, wadda ake zargin an same ta da tarin kayan zaɓe da aka rufe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), a ranar Juma’a.
KU KUMA KARANTA: Hukumar DSS ta ƙwato makamai a jihohi daban-daban biyo bayan hare-haren siyasa a Kano
Hundeyin ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Alhamis da misalin karfe 4:00 na yamma, a kan titin Candos, da ke Baruwa a unguwar Iyana-Ipaja a Legas, ya ƙara da cewa an kama wadda ake zargin ne a cikin wata cibiyar kasuwanci inda take buga takardun.
Ya ce, “An kama ta ne da kayan INEC 550 daban-daban. Laptop ɗin da ta yi amfani da shi wajen buga kayan an dawo da ita kuma ta kasa yin cikakken bayani kan yadda ta mallaki kayan.
“An mayar da shari’ar zuwa CID Yaba a Legas don ci gaba da bincike.” In ji shi.
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama wata mata ɗauke da kayan zaɓe na INEC a Legas […]
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda aka kama wata mata ɗauke da kayan zaɓe na INEC a Legas […]