Yadda aka kama ɗan kasuwa da hodar iblis mai nauyin kilogiram 9.40 a filin jirgin saman Legas

0
383

Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun cafke wani ɗan kasuwa mai suna Kingsley Celestino mai shekaru 49 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja jihar legas ɗauke da kilo 9.40 na hodar iblis wato tabar heroin da ya ɓoye a cikin jakunkuna biyu.

An kama Kingsley, ɗan asalin ƙaramar hukumar Nnewi ta kudu a jihar Anambra, a Terminal 2 na filin jirgin sama a kan hanyarsa ta zuwa Indiya ranar asabar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ta shafin ta na Facebook a ranar lahadi.

Ta ce “Rundunar hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, ta kama wani ɗan kasuwa mai suna Kingsley Celestino a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas, an kuma gano sama da kilogiram 9.40 da aka tabar tabar heroin ce da aka boye a cikin jakunkuna biyu.

“An kama Kingsley, wani fasinjan jirgin Qatar Airline a Terminal 2 na MMIA a ranar Asabar 4 ga Maris akan hanyarsa ta zuwa Indiya.

Duk da cewa ɗan asalin ƙaramar hukumar Nnewi ta kudu ne a jihar Anambra, dan shekaru 49 yana tafiya ne da fasfo din ƙasar Guinea.

“Bincike na farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana yawan tafiya Indiya akan tikitin kasuwanci, ya kuma yi ikirarin cewa yana huldar kasuwanci tsakanin Najeriya da Indiya.

An ƙara tabbatar da cewa ya samu fasfo ɗin kasar Guinea a Guinea Bissau, inda ya ce mahaifiyarsa ‘yar yankin ce.”

Leave a Reply