Ya zama dole a amince da haƙƙin Falasɗinawa na kafa ƙasarsu – Majalisar Ɗinkin Duniya

0
132

Daga Ibraheem El-Tafseer

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya zama dole kowa ya amince da ‘haƙƙin Falasɗinawa na kafa ƙasarsu.

Mista Guterres ya bayyana haka ne a taron ƙungiyar ƙasashen ‘yan ba ruwanmu da aka yi a Kampala babban birnin Uganda.

Ya ce duk wani ƙin amincewa da samar da ƙasashe biyu zai tsawaita rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas.

A ranar Alhamis da ta gabata ne firaministan Israi’la Benyamin Netanyahu ya fito fili ya ƙi amincewa da kafa da ƙasar Falasɗinawa.

Leave a Reply